Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyallen Rufe Huska Na Ci Gaba Da Zama Mai Muhimmanci


Ma'aikatan kiwon lafiya
Ma'aikatan kiwon lafiya

Akwai muhimman dalilan da yasa ya kamata a saka kyallen rufe huska a wannan lokaci fiye da kowane lokaci, a cewar cibiyar yaki da cuta mai yado a Amurka ta CDC.

Kyalle rufe huskar nada wata kariya a kan coronavirus ga mai saka shi, baicin wasu mutanen kuma dake kusa, inji wani karin bayani da cibiyar tayi.

Ya zuwa wannan lokaci, cibiyar yaki da cututtukar ta CDC, ta ce saka abin rufe huskar yana rage tofin yawu mai dauke da kwayar cuta daga mutumin da ya saka kyallen rufe huskar.

Amma bincike da dama da aka gudanar tun bayan barkewar annobar, sun nuna kyallen rufe huskar na kuma bada kariya ga wandanda ke saka kyallen daga cutar.

“Ina ganin sau tari ana kara fahimtar cewa, akwai kariya daga cutar da kyallen rufe huskar ke yi, amma ba a iya tantance adadin amfanin kyallen ba, inji wani malamin a makarantar likitanci ta Carle a jihar Illinois, William Scott,”

Tun cikin watan Afrilu, lokacin da cibiyar CDC ta bada shawarar saka kyallen rufe huska, kungiyoyi masu gudanar da bincike da dama suka yi riganganto wurin neman gano yanda kyallen ke aiki.

Amma an gano yana da matukar amfani. Binciken farko ya maida hankali ne a kan tofin yawu daga wanda ya saka kyallen. Kyallen rufe huskar na rage tofin daga kashi 50 zuwa 70 cikin dari a cewar wasu bincike da aka gudanar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG