Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LABARI DA DUMI-DUMINSA:Shugaba Buhari Ya Isa Jos


Ziyarar Shugaba Buhari a Jos
Ziyarar Shugaba Buhari a Jos

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jos fadar jihar Plato, inda zai gana da masu ruwa da tsaki biyo bayan kazaman hare haren da aka kai kauyuka hudu a yankin Gashish na Karamar Hukumar Barikin Ladi da ya janyo asarar rayuka da dama da suka hada da mata da kananan yara.

Harin da aka kai a karshen mako ya kuma janyo asarar kaddarori yayinda aka kuma raunata mutane da dama da a halin yanzu suke jinya a manyan asibitan dake Jos.

Ziyayar ta shuga Buhari tazo ne kwana daya bayanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osibajo ya kai irin wannana ziyarar inda ya gana da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin jihar Plato, sai dai masu kula da lamura sun kushewa ziyarar kasancewa bai ziyarci inda lamarin ya faru ba, bai kuma je ko da asibi daya domin ganin wandada ake jinya ba.

Ga hirar da Grace Alheri Abdu tayi da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji kafin isar shugaba Buhari.

Ziyarar Shugaba Buhari a Jos-6:40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:34 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG