Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LABARIN WASANNI: Wasan Cin Kofin Duniya


'Yan kallon gasar cin kofin duniya a Qatar
'Yan kallon gasar cin kofin duniya a Qatar

A ci gaba da fafata wasannin gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, kasar Ingila ta ragargaza Iran da ci 6-2 a wasan farko ta rukunin B a yau Litinin.

Duk da yake dai masu fashin baki na ganin cewa Ingila din ta fi karfin Iran a wasan, to amma kuma Iran din wacce ke tare da goyon bayan akasarin ‘yan kallo da ke filin wasan na Khalifa, ta fuskanci matsala ne tun a farko-farkon wasan, sa’adda ta rasa mai tsaron gidanta Alireza Beiranvand, sakamakon rauni da ya samu.

A wasa na 2 a rukunin na B kuma, yanzu haka kasar Amurka tana nan tana fafatawa da Wales.

Duk dai a yau Litinin, kasar Netherlands ta yi nasarar doke Senegal da ci 1-0 a rukunin A.

Senegal din dai na wasa ne ba tare da shahararren dan wasan ta Sadio Mane ba, wanda daga bisani aka bayyana cewa ga baki daya ba zai sami damar buga wasa a gasar ta cin kofin duniya ta bana ba.

Tun da farko dai a wasan bude gasar a jiya Lahadi, mai masaukin baki wato kasar Qatar, ta sha kashi a hannun Ecuador da ci 2-0.

Tsohon shahararren dan wasan super eagles na Najeriya Sunday Oliseh ya ce ya kamata kasashen nahiyar Afirka su dauki darasi kan sha’anin nada masu horar da ‘yan wasansu, ta hanyar la’akari da gagarumar rawar da masu horarwa ‘yan kasa suke takawa.

Oliseh ya ce kasashe 5 da ke wakiltar nahiyar Afirka a gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar Afirka ta bana a Qatar sun isa babban misali, kasancewar dukan su suna karkashin jagorancin masu horarwa na cikin gida, a maimakon na kasashen turai

Gasar cin kofin duniya
Gasar cin kofin duniya

Kasar Morocco na karkashin jagorancin dan kasar Walid Regragui, Senegal ma da kocinta dan kasa Aliou Cisse, Kamaru da dan kasar Rigobert Song, sai dan kasar Ghana Otto Addo da ke kocin ‘yan wasan kasar, da kuma Jalel Kadri dan kasar Tunisia da ke horar da ‘yan wasan kasar.

Oliseh wanda shi ma tsohon koci ne na ‘yan wasan Najeriya na Super Eagles, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake samun bunkasar masu horar da ‘yan wasa na cikin gida a nahiyar Afirka, wadanda kuma ya ce yana alfahari da su.

Makallata ‘yan kasar Japan a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta bana a Qatar, sun kuma baiwa duniya mamaki da sha’awa, a yayin da suka tsaya aikin sa kai na tsabtace filin wasa na Al Bait, jim kada bayan kammala wasan farko ta bude gasar tsakanin mai masaukin baki Qatar da Ecuador.

Kungiyar kwallon kafa ta Senegal
Kungiyar kwallon kafa ta Senegal

Ba wannan ne karon farko da ‘yan kallon ‘yan kasar Japan suke yin irin wannan karimci ba, domin kuwa ko a gasar ta cin kofin duniya ta shekara ta 2018 ma an yi ta yada hoton bidiyon su, sa’adda suke shara tare da tsaftace filin wasa, bayan wasan zagaye na 2 tsakanin Belgium da Rasha.

Duk da yake dai kasar ta su ta Japan bata sami gurbin shiga gasar ta bana ba, amma kuma hakan bai hana su ci gaba da karimcin da suka fara ba, wanda kuma bai takaita kan wasan kwallon kafa kadai ba, domin kuwa an sha ganin suna yin irin wannan a wasu wasannin na daban.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG