Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lagos Ce Birni Mafi Hatsari A Duniya - Inji Wani Rahoto


Birnin Lagos

Gwamnatin jihar Legas ta yi watsi da wani rahoto da wani sashen bincike da bin diddigi na mujallar tattalin arziki ta Landon, mai suna Economist Intelligence ta fitar, dake aiyana birnin a matsayin wanda yafi kowane birni rashin tsaro, da hatsari a duniya, daga cikin birane 60 da ta yi nazari akan su.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Gbenga Omotosho ya
fitar, ya baiyana rahoton a matsayin soki burutsu, kuma mara tushe balle
madafa.

To ko yaya al’ummar jihar ta Legas suka ji da wannan rahoto? A bayanin da suka yiwa wakilin Muryar Amurka, wasun su kamar wani malami, ya ce kokadan bai yarda da wannan rahoto ba, da a kace wai Legas ita ce mafi karancin tsaro a duniya, bayan akwai wasu jihohi da suka fi wannan jiha rashin tsaro.

A can baya ma dai an sha fitar da rahotanni makamantan wannan wanda
gwamnati da al’ummar kasa ke baiyana su a matsyain na son kai.

A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG