Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau lahadi Za'a yi Jana'izar Nelson Mandela a Mahaifarsa-Qunu


'Yan kasar Afirka ta kudu suke kallon jerin gwanon motoci ciki harda wacce take dauke da gawar Mr. Mandela.
'Yan kasar Afirka ta kudu suke kallon jerin gwanon motoci ciki harda wacce take dauke da gawar Mr. Mandela.

Dubban Mutane Ne ciki harda shugabannin kasashe ake sa ran zasu halarci jana'izar Mr. Mandela A Afirka ta kudu.

Yau lahadi ake shirin jana’izar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson mandela a mahaifarsa da ake kira Qunu, bayanda aka kai gawa can jiya Asabar. Dubban mutane ne ake kyautata zaton zasu halarci jana’izar.

‘Yan kasar dauke da tutoci ne wadanda suka fito jiya Asabar domin karramawa da ban kwana da marigayin, lokacinda motar daukar mamata dauke da gawar Mr. Mandela da aka rufe da tutar kasar, ta kamo hanya daga tashar jiragen sama dake Mthatha kan hanyar zuwa Qunu da bashi da nisa.

Wakilin MA Scott Bobb wanda yana daga cikin wadanda suka kalli wucewar jerin gwanon motocin da suke raka gawar, yace fuskokin jama’a na cike da farin ciki da kuma bakin ciki. Bobb yace wasu mutanen sun yi jiran fiye da sa’o’I takwas domin su ga wucewar jerin gwanon motocin da suka tasamma Qunu, mahaifar Mr. Mandelan. Yanzu haka dai gawarsa tana cikin gidansu dake kauyen a yankin kasar mai tuddai gabas da birnin Cape, wuri mai koren ciyayi ko da yaushe.

Ahalinda ake ciki kuma an daidaita kan rashin fahimtar juna da ta kunno kai tsakanin mahukuntan kasar da tsohon babban limamin kiristocin kasar Desmond Tutu kan halaratar jana'izar Mr. Mandela. Tutu wanda ya bayyana cewa ba zai halarci jana'izar ba saboda rashin samun takardar gayyata, yanzu yace zai halarta bayanda gwamnati tace bata turawa kowa takardar gayyata ba.
XS
SM
MD
LG