Accessibility links

Kungiyar Matasan Afirka ta Kalubali Shugabannin Afirka


Matasa da suka hasala

Yayin da take zaman karrama marigayi Nelson Mandela 'yan kungiyar matasan Afirka sun kalubali shugabannin Afirka da gaza yin irin abubuwan da Mandela ya yi.

Yayin da shugabannin duniya suka taru a filin kwallon wasa dake Sweto a Afirka Ta Kudu domin karrama marigayi shugaba Nelson Mandela su kuma shugabannin kungiyar matasan Afirka kalubalantar shugabannin Afirka suka yi domin gazawarsu a harkokin shugabanci.

A taron matasan da suka yi domin karrama shugaba Nelson Mandela shugabannin matasan sun zargi wasu shugabannin Afirka da bakin mulki na son kai da almundahana da rashin kwatanta adalci da rashin kishin kasashensu inda suka mayar da al'ummominsu bayi. Shugabannin matasan sun kwatanta Nelson Mandela a matsayin wani shugaba na karshe a wannan karnin da ya kwato 'yancin jama'arsa.

Matasan a karkashin inuwar African Youth Forum sun ce abun kunya ne a ji wasu shugabannin Afirka na yabawa Nelson Mandela da sanin ya kamata da gwarzontakarsa da son jama'arsa alhali kuwa su a zuciyarsu ba haka abun yake ba. Alhaji Ahmed Lawal ya ce shugabannin dake kan mulki yanzu a Afirka dake cewa suna juyayin Mandela yawancinsu 'yan mulkin kama karya ne, 'yan danniya masu cutar jama'arsu. Ya ce duk abun da suke fada ba gaskiya suke aiwatawa ba. Duk wanda ya hau mulki baya son ya bari. Nelson Mandela ne kadai ya hau mulki kuma ya sauka lokacin da ake bukatan ya cigaba da yin mulkin. Shi ya sauka ba tare da neman wa'adi na biyu ba. Ya ce idan wasu sun sauka basa sauka fisabilillahi. Sai abun ya kure masu suke sauka. Amma shi Mandela ya sauka ne dan ganin kansa. Ba tilasta masa aka yi ba. Ya mika milki cikin lumana da sadakar da kai. Idan gaskiya suke yi ya kamata su yi koyi da Mandela. Don haka yabon da suke yi masa bashi da anfani.

Mandela shi ya mika mulki ya ce shi ya tsufa a bari wani ya cigaba da mulkin Afirka Ta Kudu a madadinsa. Kuma har ya koma ga Allah bai sake sa bakinsa a harkokin mulkin kasar ba. Wannan shi ne shugabanci. Iyakaci shi ya bayar da shawara. Tun da ya sauka ba'a taba jinshi ya fadi wani abu game da shugaban kasar ba. Alhaji Lawal ya ce a lura da abun dake faruwa a Najeriya. Sai a ji shugaba mai ci da na da suna cacar baki. Irin wannan abun bai kamata ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

XS
SM
MD
LG