Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyi Ne Suke Marawa ‘Yan bindiga Baya – Masari


Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)
Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)

Masari ya kara da cewa, akwai lokuta da dama da ake ba da belin ‘yan fashin daji sai su koma su ci gaba da ayyukansu na ta’asa.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi kira ga kungiyar lauyoyin Najeriya ta NBA da ta hana mambobinta zuwa belin mutanen da ake zargi da ayyukan ‘yan bindiga.

Masari ya yi kiran ne yayin bikin rantsar da sabbin alkalai uku da aka yi a jihar.

“Ya kamata kungiyar lauyoyi ta NBA ta ja hankalin mambobinta kan yadda suke zuwa suna taimakon ‘yan bindiga, masu fyade da fashi, ta hanyar nema musu beli da sunan kare ‘yancin bil adama.”

Masari ya kara da cewa, akwai lokuta da dama da ake ba da belin ‘yan fashin daji sai su koma su ci gaba da ayyukansu na ta’asarsu.

“Za a iya kaucewa aukuwar irin wannan lamari idan ba a ba da belin ba.” Masari ya kara da cewa.

Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya tanadi cewa duk wanda aka kama da zargin aikata laifi na da 'yancin a ba da belinsa, ko da yake, ya danganta da irin laifin da mutum ya aikata.

Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya wacce har ila yau ita ce jihar da shugaban kasa ya fito, ta jima tana fama da matsalar ‘yan fashin daji.

A watan Agusta, gwamna Masari ya ce kananan hukumomi 10 cikin 34 da ke jihar suna fama da hare-haren ‘yan bandiga a kullum.

XS
SM
MD
LG