Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas Za Ta Daina Biyan Tinubu, Fashola Kudaden Fansho


Gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu

Gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana aniyarsa ta soke dokar nan da ta ba da damar a rika biyan tsoffin gwamnoni da mataimakansu kudaden fansho.

A shekarar 2007 aka samar da dokar a jihar wacce take ba da dama a biya tsoffin wadanda suka rike madafin iko.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da kasafin kudin 2021 a gaba majalisar dokokin jihar a ranar Talata a cewar jaridar Daily Trust.

A cewar gwamman, daukan wani mataki zai taimaka wajen rage kudaden da gwamnati ke kashewa tsoffin gwamnoni da mataimakansu.

“Mai girma shugaban majalisa da mambobin wannan majalisa, lura da bukatar ganin an rage kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati da kuma nuna sadaukarwa, za mu aiko da kuduri ga majalisa domin a soke wannan doka ta 2007.” Gidan talbjin na Channels ya ruwaito.

Ya kara da cewa, daukan matakin ya zama dole lura da yadda hanyoyin kudaden shigar jihar suka ragu.

Soke dokar na nufin za a daina biyan tsoffin gwamnonin jihar da suka hada da Asiwaju Bola Tinubu da ya shugabancin jihar daga 1991 zuwa 2007, sai Babatunde Raji Fashola wanda ya mulki jihar tsawon shekara takwas.

Sai kuma Akinwumi Ambode da ya gaji Fashola.

Gwamna Sanwo-Olu, ya gabatar da kasafin kudin na 2021 akan Naira Triliyian 1.15.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG