Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBERIA: A Karo Na Biyu Kasar Ta Rabu da Cutar Ebola -WHO


Ma'aikatan kiwon lafiya masu yaki da cutar ebola a Liberia
Ma'aikatan kiwon lafiya masu yaki da cutar ebola a Liberia

Kawo yanzu babu wani bincike daga mai'aikatar kiwon lafiya da ya nuna an samu kwayar cutar cikin kwanaki 42 da suka gabata.

Yau Alhamis Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO a takaice ta sake sanar da duniya cewa yanzu babu kwayar cutar ebola a kasar Liberia.

A sanarwar da Hukumar ta bayar yau Alhamis tace yanzu sai a sawa kasar ido nan da kwanaki casa'in, lokacin da za'a sa mata ido sosai domin koda kwayar cutar zata bullo a wani wurin da ba'a kyautata zato ba.

A ranar tara ga watan Mayu ne dai Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta sa kasar cikin wadanda basu da kwayar cutar ko cutar. To saidai ba zato ba tsammani ranar 29 ga watan Yuni hukumar ta sanar da duniya wani dan shekara 17 da haihuwa ya kamu da cutar kuma ya rasu jajiberen sanarwar.

Daga bisani kuma an sake samun wasu biyar dauke da kwayar cutar.

Idan dai ba'a manta ba lokacin da cutar tayi kamari a kasar Libeia bara mutane 4,800 ta aika lahira. Haka ma cutar ta kashe mutane da dama a kasashen Guinea da Saliyau inda ma yanzu mahukunta na cigaba da yin kokarin hana cutar sake yaduwa.

Hukumar kiwon lafiya ta yabawa gwamnatin Liberia da al'ummarta dangane da yadda suka tashi haikan suka tunkari wannan sabuwar bullar ba tare da bata lokaci ba

XS
SM
MD
LG