Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool vs Madrid: Ya Ya Kuke Ganin Wasan Zai Kaya?


Sergio Ramos da Mohamed Salah. (APTOPIX)

A yau Laraba Real Madrid za ta bi Liverpool gida, don karawa a zagaye na biyu a ci gaba da gasar neman lashe kofin Champions League na UEFA yayin da Dortmund za ta karbi bakuncin Manchester City.

Yau za a kara tsakanin Liverpool da Madrid a zagaye na biyu a wasan neman lashe kofin zakarun nahiyar turai a matakin Quarter-final.

Madrid ta lallasa Liverpool da ci 3-1 a zagayen farko a gida (Spain.)

Masu sharhi na ganin Liverpool na da jan aiki a gabanta a wasan da za a kara a zagaye na biyu duk da cewa ta yi iya bakin kokarinta a zagayen na farko.

Hakazalika, a yau ne Manchester City ta Ingila za ta gwada kaiminta da Borussia Dortmund ta kasar Jamus.

Dortmund ce za ta karbi bakuncin City a wannan wasa.

A wasan da suka kara a zagayen farko, City ta doke Dortmund da ci 2-1.

Ya ya kuke ganin wadannan wasanni za su kaya?

Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona

Gasar Premier League: Waye Zai Maye Gurbin Mourinho?

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG