Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liverpool Na Da Jan Aiki A Anfield - Masu Sharhi


Mohamed Salah

Vinicius Junior ya ci wa Real Madrid kwallo biyu, a karawar da suka yi da Liverpool a neman lashe kofin gasar zakarun turai ta Champions League.

Wasan an buga shi ne a zagayen farko a gidan Madrid inda Marco Asensio shi ma ya zura kwallo guda.

Ita dai Madrid ta yi amfani da saken da Liverpool ta yi, ta lallasa ta, ko da yake, gabanin kwallon Vinicius ta biyu, Mohamed Salah ya ci wa Liverpool kwallo daya.

Wannan wasa kusan maimacin abin da aka gani ne wasan karshe na gasar ta UEFA a shekarar 2018, wanda Madrid ta lashe kofin.

Kuma tun daga lokacin ne aka rika yin waje rod da ita tun a zagayen ‘yan 16 shekara biyu a jere.

A ranar 14 ga watan Afrilu Madrid za ta bi Liverpool Anfield don karawa a zagaye na biyu.

Masu sharhi na ganin Liverpool na da jan aiki a gabanta a wasan da za a kara a zagaye na biyu duk da cewa ta yi iya bakin kokarinta a zagayen na farko.

A gefe guda kuma wasan da aka yi tsakanin Manchester City da Dortmund , City ta lallsa Dortmund da ci 2-1.

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

AFCON 2021, Ahmed MusaQueiroz ta Masar

Queiroz ta Masar, "Ba mu kasance cikin filin wasa ba a farkon rabin lokaci 'yayin da' Najeriya ta ci nasara''
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Najeriya na atisaye gabanin wasanta na farko da Masar a rukunin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG