Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikata Sun Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Tsohon Hoto: Facebook/NLC)
Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Tsohon Hoto: Facebook/NLC)

Yunkuri na karshe da gwamnati ta yi a daren Litinin na hana ma’aikatan shiga yajin aiki ya citura, bayan da suka ki amsa wata gayyata da ma’aikatar kwadago ta aika musu.

Ma’aikata a Najeriya karkashin kungiyar kwadago ta NLC, sun tsunduma yajin aiki a yau Talata don nuna rashin jin dadinsu kan yadda rayuwa ta yi tsada tun bayan da aka janye tallafin man fetur.

Hakan na nufin yajin aikin ya sa tattalin arzikin na Najeriya wanda shi ne mafi girma a nahiyar Afirka ya shiga halin kakanikayi.

Kungiyoyin kwadagon kasar sun kuma sha alwashin ba za su janye yajin aikin ba har sai an biya musu bukatunsu.

Wannan dai shi ne yajin aikin na biyu da ma’aikatan kasar suka shiga cikin wata guda

Yunkuri na karshe da gwamnati ta yi a daren Litinin na hana ma’aikatan shiga yajin aiki ya citura, bayan da suka ki amsa wata gayyata da ma’aikatar kwadago ta aika musu.

A wata hira da yi da Muryar Amurka a kwanakin baya jim kadan bayan janye wani yajin aikin da kungiyar ta yi bayan da kotu ta dakatar da shi, Sakataren hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Comrade Nasir Kabir ya ce bukatarsu ita ce a dawo farashin mai kamar yadda yake a da.

Wannan yajin aiki na gargadi ne, inda ma'aikatan za su kwashe kwana biyu suna yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG