Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Kamfanin Man Fetur A Nijar Sunyi Zanga-Zanga Kan Fifita Ma’aikatan Kasar China A Kansu


Zanga Zangar Ma'aikatan Kamfanin Man Fetur Na CNPC A Nijar

A jamhuriyar Nijar wasu ma’aikatan kamfanin hakar man fetur na CNPC na hadin gwiwar kasashen Nijar da China, sun yi zaman dirshan a birnin Yamai domin nuna rashin amincewa da abin da suka kira fifita ma’aikatan China akan ma’aikatan kasar Nijar.

Ma’ikatan na korafi ne akan banbancin da suka ce shugabanninsu wanda akasarinsu ‘yan kasar China ne suke nuna musu akan aiki, hakan yasa sukayi zaman dirshan acewar jagoran ma’aikata Tasi’u Ibra ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka, Sule Muminu Barma.

Tasi’u yace, ana wulakanta ma’aikatan Nijar tare da nuna fifiko idan aka kwatanta da yadda ake yiwa ma’aikatan daga China, haka kuma ba a bin dokokin aikin da suka kamata, hakan yasa suka ki amincewa da wannan lamari su ke kuma neman a bi doka tare da basu ‘yancin su.

Ma’aikatan na Man Fetur ‘yan kasar Nijar sunce sun sanar da hukumomin kasar akan mawuyacin halin da suke ciki sai dai har yanzu babu wani sauyi da aka samu. Inda sukace sun rubuta a rubuce sun baiwa shugaban kasar Nijar, haka kuma sun sanar da minista mai kula da Man Fetur da minista mai kula da ‘yancin ma’aikatan Nijar.

Ma’ikatan dai sun lashi takobin ci gaba da neman ‘yancin su har sai hakkarsu ta cimma ruwa. A shekara ta 2011 ne kasar Nijar ta fara hakko man fetur daga rijiyoyin Agadem ganga Dubu 20 a kowacce rana, wadanda matatar Sonraz ke tacewa a Damagaram, domin bukatun ‘yan kasar da na kasashe makwabta kafin daga baya gwamnatin kasar ta bullo da shawarar samar da hanyoyin fitar da shi zuwa kasuwannin duniya, ta hanyar wani bututu da take tunanin shimfidawa nan gaba da hadin kan kasashen Chadi da Kamaru.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG