Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Samarda Gidaje Zata Sake Gina Gidajen da Rikicin Boko Haram Ya Daidaita


Wasu 'Yan Gudun Hijira a Jihar Borno

Jiya ce raanar muhalli ta duniya saboda haka ma'akatar samarda gidaje ta tarayyar Najeriya ta yi alkawarin sake gina gidajen da 'yan Boko Haram suka rusa suka kuma kona a arewa maso gabashin kasar

Ma'aikatar tace zata shiga jihohin da rigingimun Boko Haram ya daidaita saboda bada tata irin gudummawar.

Zata sake gina gidajen mutanen da rikice-rikicen Boko Haram suka lalata masu muhallansu.

Babban daraktan ma'aikatar Farfasa Muhammad Al-Amin ya bayyana hakan yayin bikin ranar samarda muhalli ta duniya da ake kira World Habitat Daya a turance ranar da kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kebe.

An yi bikin ne a sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Farfasa Al-Amin yace Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar ce domin tattauna matsalar muhalli da gidaje da kuma inda mutane ke zama. Saboda haka ma'aikatarsa ta ga ya dace su gudanar da taron wannan shekarar a sansanin 'yan gudun hijira wadanda rikici ya rabasu da gidajensu domin tattaunawa akan matsalolin da suke fuskanta da suka jibanci muhalli.

Yace duniya ta damu da irin halin da suka shiga musamman shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari. Da zara sun koma garuruwansu ma'aikatar da kungiyoyi da taimakon mutane zasu sake gina masu gidajensu.

Mutanen dake sansanin sun yi korafe korafe da dama akan matsi da suke fuskanta tare da yoyo da wasu dakunan ke yi idana an yi ruwan sama. Abinci bai wadacesu ba.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG