Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawar Dimokradiyar Congo Ya Rasu


Etienne Tshesikedi madugun adawar Dimokradiyar Congo da ya rasu

Jagoran 'yan adawar Congo Etienne Tshisekedi ya rasu a Brussels inda ya je jinya. Shekarunsa 84 da haihuwa.

Jam'iyyar su Tshisekedi ta Union for Democracy and Social Progress ta tabbatar da mutuwar tasa. Ya kafa jam'iyyar ce a 1982 don ja da gwamnatin dadadden mai mulkin kama-karya Mobutu Sese Seko, a kasar da a lokacin ake kiranta Zaire.

Jagoran 'yan adawar, wanda ya zama Firayim Minista sau tari a zamanin Mobutu, ya zauna a kasashen waje na tsawon shekaru da dama kafin ya koma kasar a watan Julin bara, lokacin da ya yi wani jawabi a wajen wani gangamin nuna adawa da cigaba da mulkin Shugaba Joseph Kabila.

Rasuwar Tshisekedi ta zo a wani mawuyacin lokaci ga Congo, inda 'yan adawa su ka yi ta gwagwarmaya ta tsawon watanni suna neman Kabila ya sauka daga mulki, bayan abin da 'yan adawar su ka kira 'magudin zabe.'

XS
SM
MD
LG