Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafarauta Sun Kwato Maiha daga Hannun 'Yan Boko Haram


‘Yan sintiri da Mafarauta

Mafarauta da 'yan tauri sun farma 'yan Boko Haram a jihar Adamawa sun kwato Maiha.

Maharan sun kashe na kashewa cikin 'yan kungiyar Boko Haram sun kuma fatattaki wasunsu kana suka kwace garin Maiha.

Mafarautan sun sha alwashin taimakawa jami'an tsaro domin kubutar da yankunan dake hannun su 'yan Boko Haram.

Kafin mafarautan su yunkura 'yan Boko Haram su riga sun kashe sojoji da dama har da wani kanal a yankin Maihan.

Wadanda suka fito daga yankin suna murnar abun da ya faru. Lamarin wani sabon babi ne aka bude. Yanzu wasu na cewa kamata yayi mafarauta, 'yan kalare, 'yan tauri da 'yan kato gora su hada hannu su kawar da 'yan Boko Haram daga yankunansu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG