Accessibility links

Maganar Tsaro a Taron Kasa na da Mahimmaci Inji Tsohon Mataimakin Sufeto Janaral Nuhu Aliyu


Tsohon Mataimakin Sufeto Janaral Nuhu Aliyu

Tsohon mataimakin sufeton janaral na yan sanda Nuhu Aliyu yace lamarin tsaron a Najeriya na da mahimmanci.

Tsohon mataimakin sufeton janaral din yan sanda Nuhu Aliyu yace batun lamarin tsaro a Najeriya nada mahimmanci a taron kasa da aka fara a ya'u a Abuja.

Ya fardi haka ne a wata hira da su kai yi da wakilinmu a Minna babban birnin jihar Niger, ya kara da cewa taron kasar ba zai yi wani tasiri ba sai an harda da majalisar kasa,a cewarsa wana ba shine na farko ba taron.

Ya kara da cewa majalisar kasa itace zata iya zartar da dokar da zai shafi kowa a kasar, bawai a yi rafarada kawai ba.

Shi kuma tsohon gwamnar jihar Kano Kanal Sani Bello mai ritaya yace inda har babu tsaro duk maganar da za ayi magane ce kawa.

XS
SM
MD
LG