Accessibility links

Magidanta Miliyan Saba'in Ne Suke Zaune Cikin Talauci A Najeriya


Wata mata tana rai-rayar tsaki a kudancin Najeriya.

Babban Bankin Duniya yace magidanta miliyan 70 ne suke zaune a cikin talauci a Najeriya.

WASHINGTON, D.C - Jihar Jigawa ce kan gaba a jihohin da ke fama da talauci, kuma mazauna kauyuka ne suka fi fuskantar wannan matsala.

Duk da cewa talauci ya ragu tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2010, babu alamun da ke nuna hakan.

Ibrahim Alfa Ahmed, na Sashen Hausa ya tuntubi mai baiwa Shugaba Goodluck Jonathan shawara a kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak domin jin ko wannan rahoton bai nuna gazawar gwamnatin ba?

Mr. Gulak ya ce ba zai iya "tabbatarwa" ba, kuma gwamnati na bakin kokarinta wajen rage talauci tsakanin al-umma, ta samarwa matasa dubu uku ayyuka a kowace jiha.

"Ya kamata gwamnatocin Jihohi suyi koyi da abinda gwamnatin tarayya take yi, suma su samarwa matasa kamar dubu uku ayyukanyi", in ji Mr. Gulak.

XS
SM
MD
LG