Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Gadhafi Sun Yi Zanga Zangar Mai Da Martani Ga Masu Zanga Zangar Kin Gwamnati


Magoya bayan gwamnati kenan ke zanga-zanga a Libiya.

Daruruwan magoya bayan Shugaban Libiya Moammar Gadhafi sun taru a babban birnin kasar, Tripoli, a yau Alhamis kwana guda bayan ‘yan gwagwarmayar adawa sun shirya zanga-zangar das u ka kira, “ranar nuna bacin rai”

Daruruwan magoya bayan Shugaban Libiya Moammar Gadhafi sun taru a babban birnin kasar, Tripoli, a yau Alhamis kwana guda bayan ‘yan gwagwarmayar adawa sun shirya zanga-zangar das u ka kira, “ranar nuna bacin rai” wanda kwaikwayo ne na abin da aka yi a Misra da Tunisia.

Kamfanin Dillancin Labaran Associated Press ya ruwaito wani dandalin intenet na ‘yan adawa na cewa masu zanga-zangar kin gwamnati sun jajirce duk ko da fatattakarsu da aka yi ta yi su ka kaddamar da gangami a birane hudu. A halin da ake ciki kuma kungiyar rajin kare hakkin dan adam na Human Rights Watch da ked a hedkwata a Amurka t ace jami’an tsaron Libiya sun kama akalla ‘yan gwagwarmaya 14 tun ma kafin a fara zanga-zanga.

Shugabannin adawa da ke kasashen ketare, kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam da ke Libiya da kuma ‘yan gwagwarmaya ta amfani da intanet sun yi amfani da kafafen sadarwar intanet wajen kiran zanga-zangar das u ka kira “ranar nuna bacin rai” din, bayan fafatawar da aka yi jiya Laraba tsakanin masu zanga-zangar kin gwamnati da jami’an tsaro.

Masu shirya zanga-zangar sun ce so su ke su tuna da ran 17 ga watan Fabrairu lokacin da wasu munanan al’amura biyu su ka faru a wannan zamani na Gadhafi mai tsawon shekaru 42. A ranar ce cikin 1987, Libiya ta kashe wasu matasa a bayyanar jama’a bisa zargin cin amanar kasa. A 2006 kuma, ‘yan sandan Libiya sun yi amfani da karfi fiye da kima su ka murkushe wata zanga-zanga a harabar karamin ofishin jakadancin Italiya a birnin Benghazi, har su ka kashe mutane 10

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG