Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka


Gini Majalisar Dokokin Amurka

A dai dai lokacin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ke jagorantar 'yan Majalisun Amurka biyu a bikin tabbatar da kuri'un kwaleji da zababben shugaban kasa Joe Biden ya samu a zaben Nuwamba, magoya bayan Trump cikin fushi sun afkawa Majalisar tare da dakatar da wannan biki.

Dubban magoya bayan shugaban Amurka Donald Trump da ke daga tutoci sun mamaye harabar Majalisar Dokokin ta Amurka a ranar Laraba, inda suka tilasta wa ‘yan Majalisar ficewa da tsayar da bikin da ake yi na tabbatar da kuri’un zabe, matakin karshe a zaben Joe Biden da Kamala Harris a matsayin shugaban kasa da mataimakiyarsa.

Hotunan talabijin masu ban mamaki sun nuna masu zanga-zangar na tsallakawa ginin Majalisa. Daruruwan masu zanga-zangar sun fi karfin ‘Yan Sandan dake tsaron kofar Majalisar suka kuma dunguma cikin ginin, ya yin da aka ruwaito wasu na kokarin fasa kofofin zauren Majalisar Wakilai inda‘ yan Majalisar suka yi ta muhawara game da kuri’un kwaleji da ke nuna Biden ya kayar da Trump.

Magajin gari ta birnin Washington gundumar Colombia, Muriel Bowser ta sanya dokar hana fita daga karshe shida na yamma, kuma an kira dakarun tsaron kasa na fara aiki da National Guard.

Tashar gidan talabijin ta Fox News ya dauki hotunan jami’an tsaro na farin kaya dauke da bindigogi suna fuskantar masu zanga-zanga a cikin ginin. Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar, Kevin McCarthy, memba na Jam’iyyar Trump ta Republican, ya fada wa kafar sadarwar cewa ya ji rahoton ‘yan sanda da ke cewa an yi harbe-harbe.

An harbe wani farar hula a cikin ginin Majalisar, kuma an kai shi asibiti.

XS
SM
MD
LG