Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Trump Sun Lashi Takobin Kare Shi A Batun Tsige Shi


Shugaban Kasar Amurka Donald Trump
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

Yayin da ake tsammani majalisar wakilan Amurka zata kada kuri’ar tsige shugaba Donald Trump a wannan makon, fadar White House ta maida hankalinta a majalisar dattawan kasar da ‘yan Refublikan ke da rinjaye, inda shugaban kasar zai fuskanci shari’a a farkon watan Janairu.

Shugaba Trump da mukarrabansa suna shirin ci gaba da kare shi da sauri kuma ta ko wacce hanya, tare da burin juya al’amari kan ‘yan adawa na jam’iyyar Demokrat.

A wannan makon, jam’iyyar Demokrat da ke da rinjaye a majalisar wakilan Amurka ake tsammani za su kada kuri’ar tsige shugaba Donald Trump akan tuhume-tuhuman yin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma hana ‘yan majalisa gudanar da aikinsu.

Shugaba Trump zai fuskanci shari’a a majalisar dattawan Amurka, inda ‘yan Demokrat suke so su ji daga karin wasu shaidu, cikin su har da mukaddashin shugaban ma’aikatan fadar White House, Mick Mulvaney da tsohon mai bada shawara kan tsaron kasa, John Bolton.

Yanzu da binciken yake komawa zuwa ‘yan Refublikan da ke da rinjaye a majalsiar dattawa, fadar White House ta canja dabarunta gaba daya. Suna aiki yanzu haka da jagororin 'yan Refublikan don a yi sauri a kammala shari’ar kana a rage irin barnan da zata yi a siyasance.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG