Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuncin Rayuwa Ya Sa Ina So Na Kashe Kaina – Ummi Zeezee


Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga yanayi na kuncin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar Ummi ta fadi hakan a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram.

“A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.” Ummi ta rubuta da harshen Ingilishi.

Sai dai jarumar wacce ta yi fitattun fina-finai irinsu ”Jinsi,” “Gambiza” da "Tutar So" ta ce kada kowa ya tambaye ta dalilin da ya sa take so ta aikata wannan danyen aiki.

Karin bayani akan: Kannywood, Ummi Ibrahim, Ummi Zeezee, Nigeria, da Najeriya.

“Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili me ya sa, abin da nake bukata a gare ku shi ne, addu’a.” Jarumar ta ce, wacee ta yi amfani da manyan harrufa wajen rubuta wasu daga cikin kalamanta.

Ummi ta kasance daya daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da tauraronta ya haska a farkon jerin shekarun 2000.

Ta yi fina-finai da dama da fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu, marigayi Ahmed S. Nuhu, Abba El Mustapha da Ibrahim Mai Shunku.

A lokacin da take haskawa, ta yi tashe tare da jarumai mata irinsu, Jamila Nagudu, Farida Jalal, Ummi Nuhu, Hafsat Shehu da Rashida Mai Sa’a, Rukayya Dawayya da Mansura Isah.

Sai dai daga baya an daina jin duriyarta na tsawon wasu shekaru da dama a harkar fina-finan Hausa, lamarin da wasu suke ganin ya sa tauraronta ya dishe.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG