Accessibility links

Mahara Sun Kashe Mutane Akalla 18 A Jihar Zamfara


Sojojin Najeriya su na gadin wani wurin binciken ababen hawa a Maiduguri, Jihar Borno, daya daga cikin wuraren da aka fi samun tashin hankali a kasar.

Mahara 150 dauke da bindigogi da adduna suka far ma kauyen Lingyado, suka bi gida-gida su na harbewa da sarar mutane

An kashe mutane akalla 18 a wani kauye dake Jihar Zamfara a arewacin Najeriya, a bayan da wasu mutane suka kai farmaki cikin kauyen da bindigogi da adduna.

‘Yan sanda sun fada yau lahadi cewa wadannan mahara su kimanin 150 sun dira kan wannan kauye mai suna Lingyado, inda rahotanni suka ce sun yi ta bin gida-gida su na harbewa ko sare mutane.

‘Yan sanda suka ce sun yi imanin cewa wannan harin ramuwar gayya ce ta harin da aka kai a kan wani kauyen dake yankin a watan Agusta.

Hukumomi sun tura sojoji zuwa Lingyado a wani yunkuri na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG