Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ubangiji Ya Kubutar da Bafaranshen da Aka Sace


'Yansanda na tsaro domin dakile ta'adanci

Mr Fransis Colon bafaranshe na wanda yan bindiga suka sace daga Rimi jihar Katsina shekarar da ta gabata.

Shekarar da ta gabata wasu 'yanbindiga da ake zato 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace wani Bafaranshe a garin Rimi cikin jihar Katsina.

Bayan sun sace shi sai suka wuce da shi Kano inda ya kwashe watanni tara tare da su a tsare. Daga Kano suka sake yin arangaba da shi zuwa Zaria inda a nan ma ya yi wata biyu kafin Ubangiji Ya yi masa gyadar dogo.

Mutumin mai suna Francis Colon ya samu ya arce ne lokacin da wadanda suke tsare da shi suka shiga yin sallah. Ko da ya fice sai ya tsayar da babur da ya kaishi ofishin 'yansanda mafi kusa. Daga can ne aka mika shi ga hekwatar 'yansandan dake Kaduna.

Kawo yanzu babu wanda ya san abun da 'yanbindigar suka nema awurinsa ko kuma irin aikin da ya zo yi a Najeriya har ya zauna garin Rimi cikin jihar Katsina. Binciken 'yansanda ne zai bada bayani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG