Accessibility links

Mahmoud Abbas Yace An Kaddamar Da Juyin Juya Halin Falasdinawa


Dubban Falasdinawa dauke da hotunan Mahmoud Abbas suka yi ma shugaban nasu tarbar gwarzaye, lahadi 25 Satumba, 2011 a birnin Ramallah dake yankin Yammacin Kogin Jordan.

An yi ma shugaba Abbas tarba irin ta gwarzaye yau lahadi a lokacin da ya koma Ramallah daga babban taron shekara na Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya fadawa dubban ‘yan Falasdinu a birnin Ramallah dake yankin Yammacin Kogin Jordan cewa an kaddamar da juyin juya halin Falasdinawa, a bayan mataki mai tarihi da ya dauka na mika takardar neman amincewa da kasar Falasdinu a gaban Majalisar Dinkin Duniya.

An yi ma shugaba Abbas tarba irin ta gwarzaye yau lahadi a lokacin da ya koma yankin Yammacin Kogin Jordan daga New York. A can New York din, shugaba Abbas ya sa kafa ya shure kiraye-kirayen Amurka da Isra’ila kan cewa ya watsar da yunkurin neman amincewa da kasar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya.

A maimakon haka, ya bukaci Babban Zauren taron Majalisar a ranar Jumma’a da ya amince da ‘yantacciyar kasar Falasdinu.

Kungiyar Sassa Hudu masu tuntubar juna kan Gabas ta Tsakiya, wadda ta kunshi Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Rasha, ta yi kira ga Isra’ila da Falasdinawa da su koma shawarwarin neman zaman lafiya cikin wata guda su kuma cimma kammalalliyar yarjejeniya nan da shekara mai zuwa.

Ministan harkokin wajen bani Isra’ila, Avigdor Lieberman, ya fada yau lahadi cewa yana goyon bayan shirin da kungiyar tuntubar junan ta gabatar, ya kuma yi kira ga Falasdinawa da kada su nemi bankado hujjojin kauracewa teburin shawarwari.

Ministan harkokin wajen Falasdinawa, Riyad al-Maliki, ya fada jiya asabar cewa sabon shirin komawa ga shawarwarin neman zaman lafiya da kasar Isra’ila bai kai mizanin amincewa ba a saboda bai kunshi yin kira ga Isra’ila ta daina gina gidaje ma yahudawa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye ba.

XS
SM
MD
LG