Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya Da Falasdinu Suka Mamaye Yinin Farko A Majalisar Dinkin Duniya


Tutar Libya ta asali kamin Gadhafi ya hau mulki a kasar. Jiya aka daura ta harabar majalisar dinkin duniya.

Lamura da suka mamaye wunin farko na bude taron koli na majalisar dinkin duniya jiya talata,sun hada da matakan neman kuri’u daga kasashe dake goyon bayan kafa kasar Falasdinu, da kuma kalaman karfafa goyon baya ga gwamnatin wucin gadi a Libya.

Lamura da suka mamaye wunin farko na bude taron koli na majalisar dinkin duniya jiya talata,sun hada da matakan neman kuri’u daga kasashe dake goyon bayan kafa kasar Falasdinu, da kuma kalaman karfafa goyon baya ga gwamnatin wucin gadi a Libya.

Fiyeda shugabannin kasashen duniya 100 ne suka hallara a helkwatar majalisar dake New York domin taro majalisar na shekara shekara karo na 66.

An daura tutar gwamnatin wucin gadin Libya a harabar majalisar dinkin duniya jiya talata, yayin da shugabannin duniya suka hallara domin tattaunawa kan goyawa Libya baya bayan Gadhafi yak au. Kakakin majalisar dinkin Duniya Ban ki-mmon ne ya jagoranci zaman kwamitin tuntuba kan Libya,yace irin kalubale da Libya take fuskanta suna da yawa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya baiwa shugabannin Libya tabbacin Amurka zata kasance “kawa” wacce zata taimaka musu wajen habaka tsaro, ayyukan jinkai, da kuma ci gaba da komawa kan turbar demokuradiyya cikin lumana.

Shugaban majalisar wucin gadin kasar, Mustafa Abdel Jalil ne, ya wakilci kasarsa.

Abu na biyu da ya cike tattaunawar da ake yi a majalisar shine batun Falasdinu. Ministan harkokin wajen yankin Falasdinu Riad al-Malki yayi kira ga Amurka ta sake tunanin alkawari da ta yi cewa zata hau kujerar naki, idan Falasdinu ta gabatar da bukatar neman majalisar ta amince mata zama kasa mai cin gashin kai.

Duk da rashin amincewar Amurka da Isra’ila kan wan nan yunkuri, al- Malki, ya bayyana kwarin guiwar gwamnatin yankin zata sami kuri’u tara cikin 15 dake kwamitin sulhun. Ranar jumma a ce ake sa ran shugaba Mahmodu Abbas zai gabatar da bukatar haka, a lokacin ne ake sa ran zai yi jawabi ga babban zauren Majalisar dinkin duniya.

A jiyan ne kuma ake sa ran wakilan kasashe takwas masu arzikin masana’antu zasu zauna domin tsara matakan bada tallafin tattalin arziki da na siyasa ga gwamnatocin kasashen larabawa da suke kokarin bin tafarkin Demokuradiyya. Kasashen da zasu ci gajiyar wan nan shiri sun hada da Tunisia, Masar, Moroco, Jordan, da kuma ‘yar auta Libya. Wakilan wadan nan kasashe zasu gana da minsitoci daga kasashen masu arzikin masana’antu da kuma wasu kasashe dake gabas ta tsakiya domin tattaunawa kan sabuwar marran siyasa a yankin.

Haka ma batutuwa na cututtuka da basa yaduwa, da abinci mai gina jiki, samun makamashi mai inganci da sare dazuka suna daga cikin lamura d a aka tatttauna akansu a jerin tarurruka da aka yi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG