WASHINGTON D.C. —
Shugaban Hukumar lafiya ta duniya wato WHO Tedros Ghebreyesus a jiya Laraba ya fadi cewa adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a fadin duniya ka iya kai wa miliyan 10 a mako mai zuwa.
Yankin Amurka na Latin ya zamo sabon yankin da annoabar sabuwar cutar ta coronavirus ta fi kamari, inda adadin mace-macen da aka samu ya zarta 100,000.
Ko da ya ke, Amurka na ci gaba da kasancewa a gaba a adadin masu cutar a duniya, inda aka samu fiye da mutum miliyan 2.3 da suka kamu da cutar, kashi 1 cikin 4 na adadin da ake da shi a fadin duniya a cewar kididdigar jami’ar Johns Hopkins.
Har ila yau kuma Amurka ce kan gaba a mace-macen da aka samu inda sama da mutum 121,000 suka mutu a kasar.
Facebook Forum