Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Matasa Da Masu Lafiya Sai 2022 Zasu Sami Rigakafin COVID-19: WHO


Hukumar Lafiya Ta Duniya, wato WHO, ta ce mai yiwuwa matasa da mutane masu lafiya za su jira zuwa shekarar 2022 kafin ayi musu allurar rigakafin COVID-19. Dalilin haka shi ne aga cewa allurar ta wadaci masu tsananin bukatarta.

Shugabar masana kimiyya ta hukumar ta WHO, Soumya Swaminathan ta fada yau Alhamis cewa hukumomin lafiya za su ba da fifiko ga batun kiwon lafiya da ma’aikatan da suka fi fuskantar annobar, kamar jami’an tsaro da masu bada agajin gaggawa, sannan tsofaffi.

Swaminathan ta ce, tana fatan za a samu akalla allurar rigakafi coronavirus daya mai inganci zuwa 2021, amma ta ce ba za ta wadatar ba.

Ana sa rana allurorin rigakafin COVID-19 sama da 170 suna matakai daban daban na gwaje gwaje a duk duniya, ciki har da guda 10 da suka shiga mataki na karshe, da ake gwadawa a kan mutane da yawa.

Babban kamfanin harhada magunguna na Amurka Johnson & Johnson da AstraZeneca sun dakatar da gwaji na matakin karshe na baya bayan nan na allurar rigakafin, bayan da daya daga cikin wadanda ake gwada maganin akansu ya kamu da rashin lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG