Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Messi Ya Buga Wasan Karshe A Barcelona


Lionel Messi

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa, Messi bai fita atisaye a ranar Juma’a ba.

Barcelona ta ba zakaran dan wasanta Lionel Messi iznin ya tsallake wasan karshe na kungiyar a wannan kakar wasa ta gasar La Liga.

Barcelona za ta kara ne da Eibar a wasan nata na karshe.

Kungiya ta fita daga cikin rukunin masu hankoron ganin sun lashe kofin gasar.

A ranar Juma’a kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki da nufin baiwa Messi hutu gabanin gasar Copa America da ke tafe.

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa, Messi bai fita atisaye a ranar Juma’a ba.

Kwangilar Messi za ta kare ne a karshen wannan kakar wasa, kuma bai nuna wata alamar zai sabunta ta ba.

Dan shekara 33, Messi ya kwashe daukacin rayuwarsa ta kwallo ne a kungiyar ta Barcelona, ko da yake, ya yi yunkurin barinta a kakar wasa ta shekarar 2019-20, bayan da ya nuna cewa ba ya jin dadin inda kungiyar ta dosa.

A ranar 13 ga watan Yuni za a fara gasar ta Copa America, inda Argetina za ta fara karawa da Chile.

Barcelona ta kasance ta uku a teburin gasar ta La Liga, wato akwai maki bakwai kenan tsakaninta da Atletico Madrid sai kuma maki biyar tsakaninta da Real Madrid.

Akwai kuma yiwuwar Sevilla wacce maki biyu kacal ya raba su, ta tsallaka zuwa gurbi na uku yayin da take shirin karawa da Alves a gidanta.

Tuni kungiyar Eibar, wacce za ta kara da Barcelona a wasan karshen, ta shiga rukunin ‘yan dagaji.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG