Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Trump Na Da Isassun Kuri’un Da Za Su Wanke Shi


Mafi yawan ‘yan Republican a majalisar dattawan Amurka sun kada kuri’a jiya Talata game da kin amincewa da gudanar da shari’ar tsige tsohon shugaba Donald Trump.

An kada kuri'ar ne akan ko ya tunzura tarzomar da aka yi a ginin majalisa dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu ko a’a, wanda hakan ke nuna cewa mai yiwuwa ya na da isassun kuri’un da za su sa a wanke shi.

'Yan majalisa 55 ne suka goyi bayan a ci gaba da shari’ar, 45 kuma ba su amince ba, amma ‘yan Republican biyar ne kadai suka hadu da dukkan ‘yan Democrat 50.

Ana bukatar kuri’u kashi biyu cikin uku don yanke hukunci, wanda zai bukaci ‘yan Republican 17 su juya wa Trump baya, idan aka kaddara cewa ‘yan Democrats duk za su jefa kuri’a baki dayansu, bayan sun saurari karar da aka shigar akan tsohon shugaban a lokacin da za a fara shari’ar a ranar 9 ga watan Fabrairu.

Wani mai goyon bayan Trump, Sanata Rand Paul daga jihar Kentucky, ya tilasta kada kuri’a akan ko a ci gaba da shari’ar ko a’a, ya na mai kiranta “shirme da ta saba wa kundin tsarin mulki.”

XS
SM
MD
LG