Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh Ya Rasu Sanadiyar Cutar Sankara


Mai Zanen Kaya Virgil Abloh Ya Rasu Sanadiyar Cutar Sankara
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:18 0:00

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh Ya Rasu Sanadiyar Cutar Sankara

A ranar Lahadi kamfani na LVMH (Louis Vuitton Moet Hennessy) da kuma kamfani mallakar sa na Off-White , da ya kirkiro a 2013.

Mai Zanen kaya Virgil Abloh, Jagora a fannin zanen kwalliya wanda ake kwantata shi da Karl Lagerfeld na zamanin sa , ya rasu sanadiyar cutar sankara. Ya mutu a shekara 41, an sanar da mutuwar Abloh ne a ranar Lahadi daga LVMH Louis Vuitton da lakabin Off White, iri da ya kirkiro. A cikin sanarwar da iyalan Abloh suka wallafa a shafin Instagram din sa sun ce an gano Abloh n dauke da cutar sankarar zuciya a 2019, Cutar sankarar da ba’a cika ganin irinta ba a inda wani qari a cikin zuciya. Ya mutu ya bar mata daya Shannon abloh da yara biyu Lowe and Grey.

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh
Mai Zanen Kaya Virgil Abloh

A ranar Lahadi kamfani na LVMH (Louis Vuitton Moet Hennessy) da kuma kamfani mallakar sa na Off-White, da ya kirkiro a 2013. Abloh shine daraktan fasaha na kayan sawan maza na Loius Vuitton, amma kasancewar abokantaka da abokan ciniki cikin al’ada ya kasance mai fadi da kuma kuzari. Wasu suna kwatanta shi da jeff Koons. Wasu kuma suna kwatanta shi da Karl Lagerfeld na zamanin sa.” Mun yi girgiza sosai bayan da muka samu mummnan labari. Virgil ya kasance ba haziki a zane-zane, mai hangen nesa, Ya kasance mutum ne halayya mai kyau da kuma hikima babba. A cewar ”Bernard Arnault Ciyaman kuma shugaba na LVMH.

A sanarwar da Iyalan Abloh suka wallafa a shafinsa na Instagram sun ce an gano Abloh n dauke da cutar sankarar zuciya a 2019, Cutar sankarar da ba’a cika ganin irinta ba a inda wani qari a cikin zuciya.

“Ya Zabi ya jure ya yaki wannan cuta cikin sirri tun 2019, ya yi fama da kalubale iri-iri na jinya, yayinda yake taimakawa wa wasu muhimman cibiyar fasahar zane da al’adu,” a cewar sanarwar.

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh
Mai Zanen Kaya Virgil Abloh

A shekarar 2018 Abloh ya zamo darakta mai fasaha, kuma bakar fata na farko a kamfanin kayan sawan maza na Louis Vuitton a tarihin gidan zane na fasaha. Dan asalin Ghana haihuwar Amurka wanda mahaifiyar shi ta koya mishi dinki, Abloh bashi da wani horo na dinkunan zamani amma kuma yana da shaidar digiri a fannin injiya da digiri na biyu a bangaren zan-zane.

Abloh, wanda ya girma a Rockford, Illinois, a wajen Chikago, sau da yawa ana kiransa a matsayin mutum mai farfado da duniyar kayan kwalliya na zamani. Ya haskaka a matsayin DJ. Amma a cikin kankanin lokaci, sai ya fito a matsayin daya daga cikin masu bushara na masu zanen kaya. Ya kira kan sa da “ mai yi” an sanya sunan sa a jaridar Time Magazines cikin mutane suka shahara 2018.

A 2019, Abloh ya hadu da Kanye West- yanzu an fi sanin shi da Ye- lokacin da yake aiki a shagon buga kaya. Bayan da shi da Ye suna sanin makamar aiki a LVMH irin Fendi. Abloh shine Daraktan Ye. Abloh shine daraktan zanr a 2011 Ye Jay-Z kundin wakokin na “Watch the Throne,” wanda shi abloh aka gabatar da sunan shi doin bashi kyautar girmamawa ta Grammy.

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh
Mai Zanen Kaya Virgil Abloh

Aikin Abloh da west ya zama kamar wata taswira a zaman tsani zuwa mataki na gaba da ya hada gwuiwa da samun kalubale. Da Nike kuwa ya hada da kamfaninsa na Off-white label sun kera takalma na yayi da salo iri-iri da Helvita Fonts. Abloh ya kuma zana kayan daki Wa kamfanin IKEA, kwalabe wanda za iya sake cikawa wa kamfanin Evian and da manyan kwalayen saka abinci na McDonalds. An nuna ayyukanshi na fasaha a Louvre da Gagosian, da kuma wajen ajiye kayan tarihi na zamani.

Mutuwar Abhor ya girgiza duniyar nishadi. Dan wasan kwaikwayo Riz Ahmad ya fadi a shafinsa na tweeter cewa abloh “ya mikar da al’ada ya kuma canza wasan. Jeff Staple mai zanen kaya ya rubuta kamar haka “Ka koya mana yadda ake mafarki.” Pharrell Willaims kuma yace “mai kirki, kyauta, tunani da kuma hazaka.”

Abloh ya dauki kasha uku na tsarin zanen kaya- cewa sabon za’a iya yin sabon zane wajen canza kasha 3 daga abu na asali. Masu suka sun ce Abloh ya fi kokari wajen maimaitawa akan kirkiro sabon abu. Amma salon Abloh ya zama alamun na sanin kai a gareshi – da daukaka.

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh
Mai Zanen Kaya Virgil Abloh

“Streetwear in my mind is linked to Duchamp,” Abloh ya gaya waw ani mazaunin New York a 2019. “wanna tunani na kayan da aka riga aka dinka. Ina Magana akan gabashin New York kamar hip-hop ne. misali ne. Ina daukar James Brown, ina gyarawa kuma in maida sabuwar waka.

Taurari sun saka kaya daga Abloh. Beyonce, Micheal B Jordan, Kim Kardashian West, Timothee Chalamet da kuma Serena Willaims sun saka kayanshi. Kamfanin Abloh na Off-White label, Wanda LVMh yake da hannun jari cikin farkon shekarar nan, ya sanya shi mai yanke hukunci. Amma kuma nadin nashi a Louis Vuitton din ya sanya Abloh kaiwa koli a masana’antar inda a da shine bare a ciki. Abloh ya zama daya daga bakar fata shugaba mai karfi a tarihin duniyar fasahar zanen kaya.

Kamar yadda Abloh ya shirya wajen nuna rigar maza a 2018, ya fadawa GQ, “na san ina da dandali da zan iya canza masana’ata.”

Mai Zanen Kaya Virgil Abloh
Mai Zanen Kaya Virgil Abloh

“Mu masu zanen kaya, za mu iya fara yayi, zamu iya bayyana batutuwa, za mu kuma iya saka mutane da yawa su mayar da hankali akan wani abu ko kuma mu saka mutane su mayar da hankali akan mu.” Abloh yace. “bani da shaawar a nan gaba. Bani da sha’awar in yi anfani da dandalina ya zama daya da cikin kananan kungiyar bakar fatar Amurka da za su tsara gida, don nau’in nuni ta hanyar waka.

Abloh ya bar matar sa Shannon da yaransa Lowe da Grey.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG