Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Na Ci Gaba Da Karban Shaidu A Kan Binciken Tsige Trump


Masu Shaida Gaban Majalisa

A cikin wannan makon ne za’a saurari shaidu da yawa a binciken yuwuwar tsige shugaban Amurka Donald Trump a bainar jama’a.

Za’a fara sauraren ne da sanyin safiyar nan ta Talata tare da shaidu uku da kuma abin da suka sani akan zargin da ake yiwa shugaba Trump na yunkurin tursasawa Ukraine ta binciki abokan hamayyar siyasarsa.

Duka dai, kwamitocin Majalsir Wakilan za su saurari shaidu tara ne a lokacin zama biyar daban daban da za’a yi a yau Talata da Laraba da kuma Alhamis na wannan makon.

Sai dai shaidar da aka fi saka ido za ta zone daga jakadan Amurka a kasashen Tarayyar Turai da ya bada gudummuwar dala miliyan daya ga kwamitin shirye shiryen rantsar da shugaba Trump, Gordon Sondland.

Da alama Sondland ya taka rawar gani a tattaunawar tare da Ukraine akan zargin da ake yi cewa shugaba Trump ya bukaci Ukraine ta binciki wanda ake ganin zai kalubalance shi a zaben shugaban kasa na 2020, kuma tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, akan cin hanci.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG