Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Borno ta Dage Zama Har Wata Guda Bisa Zargin Cin Zarafin Wakilanta


BORNO: Sanata Muhammad Ali Ndume, Borno South

Majalisar jihar Borno ta dakatar da zamanta har tsawon wata guda bisa zargin da ta yi cewar ana cin zarafin wakilanta a cikin wannan lokaci. Matakin da majalisar ta dauka ya biyo bayan tuhumar da wakilin mazabar Damboa Habu Daja ya yi cewar Sanata Ali Ndume ya mareshi.

Yayin da wasu yan Damboa ke musunta wannan batu, Alhaji Gaje Damboa da wannan abu ya faru a gabansa ya tabbatar da faruwar haka. Bangarorin biyun sun kira tarukan manema labarai don karyata ko kuma gaskata wannan Magana.

Kakakin majalisar jihar Borno Abdulkareem Lawan da ya sanar da dage zaman majalisar, yace ba zai yi Karin bayani ba ga manema labarai, saboda ya samu shawara daga gwamnan jihar Bornon Kashim Shattima wanda yace dashi ya yi shuru a yanzu.

Kimanin watanni hudu da suka wuce wasu suka yiwa wani wakilin majalisar mai wakiltan mazabar Kwaya Kusar Muhammed Sale Banga duka amma majalisar ba tace uffan ba akai, sai a wannan karo ne wakilan majalisar suke ganin yakamata su dauki matakin kare kansu a wannan lokaci.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG