Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Amince Da Zabin Tillerson


Rex Tillerson a lokacin da bayyana a gaban Majalisar Dattawan Amurka domin a tantance shi a birnin Washington, Jan. 11, 2017.
Rex Tillerson a lokacin da bayyana a gaban Majalisar Dattawan Amurka domin a tantance shi a birnin Washington, Jan. 11, 2017.

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da zabin Rex Tillerson, tsohon shugaban kamfanin mai na Exxon Mobile a matsayin Sakataren Harkokin Wajen Amurka.

An amince da zabin na Tillerson ne bayan takun-saka da aka yi ta yi tsakanin ‘yan jam’iyar Republican da takwarorinsu na Democrat, wadanda suka yi ta haifar da tsaiko a zabin na Tillerson.

Uku kacal daga cikin ‘yan majalisar Democrat da kuma wani dan majalisa mai zaman kansa ne suka hada kai da ‘yan Republian suka zabi Tillerson, wanda aka tabbatar mai da mukamin bayan da aka kada kuri’a.

‘Yan malisar Dattawa 56 suka zabe shi yayin da 43 kuma suka nuna adawarsu, bayan da aka kwashe makwanni ana tantama kan alakar dake tsakanin Tillerson da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

XS
SM
MD
LG