Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Fadada Takunkumi Kan Iran


Majalisar Dattawan Amurka

Majalaisar dattijan Amurka ta amince da kudurin doka da ta fadada takunkumi kan Iran, dokar da wakilai daga duka jam'iyun siyasar Amurka biyun suka ce tana da muhimmanci wajen tabbatar da yarjejeniyar da kasa da kasa ta kulla da Farisa kan shirin Nukiliyar kasar.

Wakilai 99 ne suka amince da kudurin. Senata Bernie Sanders dan indipenda mai wakilatar jahar Vermont ne kadai bai jefa kuri'a ba. Kudurin ya sami amincewar wakilai 419, wakili daya bai amince ba, lokacinda majalis wakilai ta yi muhawara kan kudurin cikin watan jiya.

Wakilai daga jam'iyun duka biyu sun ce tilas Amurka ta ci gaba da sa ido sosai kan Iran saboda halayyarta na neman tsokana da kuma neman fadada karfinta a fadin yankin gabas ta tsakiya.

Jami'an Iran sunyi Allah wadai da dokar, suka ce ta sabawa yarjejeniyar da Amurka da sauran manyan kasshen duniya suka kulla da kasar kan shirin Nukiliyarta.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG