Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Congo Ta Binciki Jami'an Tsaronta


Masu zanga zanga a Jamhuriyar Dimukradiyar Congo yayin da jami'an tsaro ke sa ido akansu
Masu zanga zanga a Jamhuriyar Dimukradiyar Congo yayin da jami'an tsaro ke sa ido akansu

Babban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yancin dan adam, ya bukaci gwamnatin Jamhuriyar Dimukradiyar Congo, da ta binciki zargin cin zarafin da aka ce wasu jami'an tsaron kasar sun yi wa wasu masu zanga zanga.

Ofishin kula da 'yancin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi jami'an tsaro kan yadda suke cin zarafin bil adama, kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka Lisa Schlein ta ruwaito.

Hukumar ta ce jami'anta na bin sawun abin da ke faruwa kuma an samu akalla mutane 6 da aka kashe kana aka jima wasu 68 rauni cikin masu adawa da gwmanatin shugaba Joseph Kabila.

Ana zargin jai'an tsaron a zanga zangar adawa da gwamnati da ake yi a birnin Kinshasa.

Ofishin ya ce, jami'an na amfani da harsashi mai kisa a duk lokacin da suke kai wa masu zanga-zangar hari.

Yanzu haka gwamnatin ta tsare mutane har 121, kuma bayanai sun yi nuni da cewa an yi amfani da hayaki mai sa kwalla a wurare daban-daban ciki ko har da coci da ma wasu sassan kasar.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG