Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Ce Miliyoyin Mutane a Gabashin Afirka Na Bukatar Tallafin Abinci


'Yan gudun hijirar matsalar farin Somaliya

Hukumar Samar Da Abinci ta Duniya ta ce ta na sa ran mutane miliyan 10 ne za su bukaci agajin kayan abinci

Hukumar Samar Da Abinci ta Duniya ta ce ta na sa ran mutane miliyan 10 ne za su bukaci agajin kayan abinci, a daidai lokacin da fari mafi muni cikin tsawon shekara da shekaru ke addabar yankin gabashin Afirka.

Farin ya fi tsanani ne a mahadar kasashe uku: wato Somalia, da Kenya da Habasha. Ya haddasa gudun hijirar dinbin mutanen da ke fama da tsabar yunwa, ta yadda ya janyo kafa sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya.

Sansanin Dadaab da ke arewa maso gabashin Kenya, da aka gina don mutane 90,000, a yanzu na dauke da ‘yan Somaliya sama da 380,000 kuma dubban karin ‘yan gudun hijira ne ke kwarara zuwa wurin kulluyaumin. Shugaban Hukumar ‘Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci wurin ran Lahadi. Daga bisani ya gaya wa manema labarai cewa ana bukatar gagarimin gudunmowa don kawar da wannan annoba mafi muni a duniya.

Kungiyoyin kasa da kasa na fuskantar matsaloli wajen samar da tallafi ga wadanda su ka cigaba da kasancewa a Somaliya, wadda bat a da cikakkiyar gwamnati wadda kuma tsattsaurar kungiyar tawayen Islama, al-Shabab ta mamaye.

XS
SM
MD
LG