Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta fara babban taronta na shekarar 2017


Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugabannin duniya sun fara isowa birnin New York da ke Amurka, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran batun gwajin makamin nukiliyan Korea ta Arewa shi zai mamaye batutuwan da za a tattauna a kai.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya yana shirin gudanar da taronsa na shekara shekara kuma shugabanni da wakilai daga kasashe mambobi 193 sun fara isowa.

Shingaye da aka datse hanya dasu basu kawo cikas ga harkokin kasuwanci ba, acewar wani mai sayar da abinci a kan keke a cikin birnin New York da yake aiki a kusa da wurin taron a cikin yan watanni.

Matakan tsaro a duniya, ciki har da barazanan shirin makamin nukiliya na Korea ta Arewa, wanda yake cikin zukatan mahalartan taron na wannan mako.

A cikin batutuwa da babban taron zai tattauna akai, akwai batun dubban daruruwar musulmin Rohingya da suke arcewa daga birnin Rakhine na Myammar zuwa Bangladesh don kaucewa tashin hankali.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG