Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Gargadi Dakarun Kiyaye Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu


Dakarun Kiyaye Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu
Dakarun Kiyaye Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sakamako mai tsananin zai biyo baya, muddun ta tabbatar kamar yadda aka yi zargi jiya Laraba cewa dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ta Kudu sun kasa kare matan da ake wa fade, a wajen harabar da Majalisar ta ware don kare farar hula.

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq, ya gaya ma manema labarai a birnin New York cewa ba da wasa ba MDD ke daukar zargin cewa dakarun kiyaye zaman lafiyar ba su taimaki farar hula ba a lokacin bukata ba, ya kara da cewa kwamandan MDD a Sudan Ta Kudu na nazarin al'amarin.

Kafar jaridar Associated Press ta ruwaito shaidun gani da ido da shugabannin jama'a na cewa sojojin gwamnatin Sudan Ta Kudu sun yi fade ma mata da 'yan matan Nuer da dama a makon jiya daura da rukunin gidajen MDD, inda su ka nemi mafaka daga fadace-fadacen baya-bayan nan da aka yi a babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG