Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Bama Bamai A Mogadishu


Amurka tayi Allah wadai da kakkausar murya da tashin wasu boma bamai biyu a kofar shiga filin jiragen sama dake birnin Mogadishu a safiyar jiya Talata, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 13.

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka Ned Price, ya fada a jiya Talata cewa “Amurka na tare da kawarta Somaliya wajen yaki da ta’addanci, wanda ke kokarin kawo rashin zaman lafiya ga kasar.” yace Amurka na nan kan alkawarinta na ci gaba da taimakawa cigaban Samaliya a hanyarta ta samun zaman lafiya da kuma dakile kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kungiyar Al-Shabab mai alaka da kungiyar ta’adda ta al-Qaida, ta dauki alhakin harin ta gidan radiyonsu na Andalus. Baki daya mutane 13 da suka mutu sojojin majalisar dinkin duniya ne, a cewar jami’an tsaro.

Kofar da aka kai wannan harin,ita ce ma’aikatan filin saukar jiragen saman suka fi amfani da ita, kuma tana da kusanci da ginin da majalisar dinkin duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka suke.

Mazauna yankin suka ce sunji karar fashewa wani abu mai karfin gaske har sau biyu, da missalin karfe 9 na safiyar jiya Talata.

XS
SM
MD
LG