Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Neni A Yi Sulhu a Yemen


Jami'in aikin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Jamie McGoldrick a.
Jami'in aikin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Jamie McGoldrick a.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga bangarorin dake rikici a Yemen su nemi hanyar samun masalaha domin kauce jefar al’ummar kasar cikin wani halin kunci

A cikin wata doguwar sanarwa da membobin kwamitin duka goma sha biyar suka amince da ita, an bayyana matukar damuwa akan barkewar cutar kwalara kwanan nan, da kuma yiwuwar fuskantar yunwa.

Kwamitin sulhun ya jadada cewa, za a iya warware rikicin na kasar Yemen ne kawai ta wajen komawa gudanar da harkokin siyasa dake damawa da kowa, tare kuma da kira ga bangarorin dake rikici da juna su dauki matakan wanzar da zaman lafiya, bisa ga sanarwar da shugaban kwamitin sulhun Sacha Llorentty na kasar Bolivia ya karanta.

Yunkurun Majalisar Dinkin Duniya na wanzar da zaman lafiya ya gamu da cikas, inda makonni biyu da suka shige, manzon musamman na babban magatakardar Majalisa Dinkin Duniya ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki a rikicin har yanzu basu shirya daukar matakan da suka kamata na cimma matsaya ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG