Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah-wadai Da Harin Zamfara


Antonio Guterres

Babban sakataren ya bukaci mahukuntan Najeriya da su tashi tsaye wajen ganin an gurfanar da wadanda ke da alhakin wadannan munanan laifuka a gaban kotu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da aka kai a karshen mako a jihar Zamfara da ke Najeriya inda aka kashe fararen hula da dama.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Stephane Dujarric, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutane 200 ko sama da haka ne aka kashe a kauyukan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, yayin da wasu ‘yan bindiga suka mai da martani, sakamakon mummunan harin da sojojin sama suka kai wa maboyarsu.

‘Yan bindigar sun kai farmaki ne zuwa kauyuka biyar a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum daga ranar Talata zuwa Laraba inda suka bar wajen jina-jina.

‘Yan fashin sun kona kauyukan biyar, inda suka kashe mutane da dama tare da daddatse gawarwakinsu.

Ya zuwa safiyar Asabar din karshen makon da ya gabata, an yi jana'izar mutane 200.

Babban sakataren ya bukaci mahukuntan Najeriya da kada su rage kwarin gwiwa wajen ganin an gurfanar da wadanda ke da alhakin wadannan munanan laifuka a gaban kotu.

Guterres ya jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga gwamnati da al'ummar Najeriya a yakin da suke yi da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.

XS
SM
MD
LG