Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Farin Cikin Yadda Aka Yi Zabe A Guinea-Bissau


Wasu yara su na kallon jami'an zabe su na kidaya kuri'u ta gilashin ginin hukumar a Bissau, babban birnin kasar Guinea-Bissau, Lahadi 18 Maris, 2012.

Sai dai kuma a bayan zaben, wasu 'yan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar leken asirin sojan kasar, Samba Diallo

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Guinea-Bissau ta ce majalisar da sauran kungiyoyi na kasa da kasa sun yi farin ciki sosai da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa, yayin da ma’aikatan zabe suke ci gaba da kidaya kuri’u a wannan kasa da ta sha fama da juye-juyen mulki a Afirka ta Yamma.

Wani kakakin ofishin Wanzar da zaman lafiya na Majalisar a Guinea Bissau, Vladimir Monteiro, ya fadawa Muryar Amurka cewa mutane kalilan suka fito da safe domin wannan zabe na jiya lahadi, amma daga bisani jami’an zabe sun samu nasarar janyo jama’a suka fito domin yin zabe.

Ana sa ran samun sakamakon zaben nan da mako daya.

Masu jefa kuri’a su na fata sabon shugaba zai kawo kwanciyar hankali da dorewar al’amura a wannan kasa wadda fataken muggan kwayoyi suka mayar zango na fataucin hodar iblis ta Cocaine, inda kuma shugabannin farar hula da soja suke tsama da junansu kan ikon mulki.

Majiyoyin tsaro a kasar ta Guinea-Bissau sun ce sa’o’I a bayan da aka rufe rumfunan zabe jiya lahadi, wasu ‘yan bindiga sun je sun kashe tsohon shugaban hukumar leken asiri ta soja, Samba Diallo, wanda ya shafe watanni yana tsare a bayan wani tunzurin soja a watan Afrilun 2010.

Wadanda ek kan gaba sun hada da tsohon shugaba Kumba Yala wanda sojoji suka hambarar a wani juyin mulki a 2003, da kuma Carlos Gomez Junior, wanda yayi murabus daga mukamin firayim minista domin domin yayi takarar shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG