Accessibility links

'Yan Guinea-Bissau Su Na Zaben Sabon Shugaban Kasa Yau


Kyamfe na yakin neman zaben shugaban kasa a Guinea-Bissau

Ba a taba samun zababben shugaban da ya kammala wa’adinsa na shekaru 5 a kan karagar mulki a kasar ba.

Masu jefa kuri’a a kasar Guinea-Bissau wadda ta yi ta fama da juye juyen mulki a Afirka ta Yamma, su na zaben shugaban kasa a yau lahadi.

‘Yan takara guda tara ne suke neman shugabancin wannan ‘yar karamar kasa wadda ta samu ‘yanci daga kasar Portugal a shekarar 1974.

Tun daga lokacin kasar Guinea-Bissau ta yi fama da shugaba mai mulkin kama karya, da juye juyen mulki har uku da kuma kisan gillar da aka yi ma shugaban kasar a 2009. Ba a taba samun zababben shugaban da ya kammala wa’adinsa na shekaru 5 a kan karagar mulki a kasar ba.

Wanda zai lashe zaben na yau lahadi zai gaji marigayi shugaba Malam Bacai Sanha, wanda ya mutu a watan Janairu bayan ya jima yana fama da rashin lafiya, kuma shekaru uku bayan da aka zabe shi shugaban kasa.

Da ma tsarin mulki ya tanadi gudanar da zabe cikin kwanaki 90 domin maye gurbin shugaban da ya rasu.

Masu jefa kuri’ar su na fatar sabon shugaban kasa zai iya kawo kwanciyar hankali da dorewar al’amura a wannan kasa wadda a yanzu fataken muggan kwayoyi suke amfani da ita a matsayin zangon fataucin hodar iblis ta Cocaine, inda kuma a yawancin lokuta ake samun tsama ta mulki a tsakanin shugabannin fararen hula da na soja.

Wadanda ke kan gaba sun hada da tsohon shugaba Kumba Yala, wanda aka hambarar a wani juyin mulki a 2003, da kuma Carlos Gomez Junior wanda yayi murabus daga kan kujerar firayim minista domin ya nemi ta shugaban kasa.

Idan babu dan takarar da ya samu fiye da rabin dukkan kuri’un da za a jefa a zaben yau, za a sake zagaye na biyu na fitar da gwani a wata mai zuwa.

‘Yan kallo da yawa daga kasashen waje su na sanya idanu a zabenb na yau.

XS
SM
MD
LG