Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kira ga Hukumomin DR Congo Su Mutunta 'Yancin 'Yan kasar


Masu zanga zanga a DR Congo
Masu zanga zanga a DR Congo

Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta zargi 'yan sandan Demokaradiyar Jamhuriyar Congo da kai hari a kan masu zanga zangar lumana, lamarin da ya faru kafin shiga harkokin yakin neman zaben kasar da aka dade ana jiran gani.

Ofishin hukumar kare hakkin bil adma ta MDD, ya nuna matukar damuwa ga yanda 'yan sandan Congo suka yi amfani da karfin tuwo a kan masu zanga zanga da suka hada da kungiyoyin jama’a da jami’iyyun adawa.

Mai magana da yawun hukumar kare hakkin bil adamar, Ravina Shamdasani, tace hakan na faruwa ne, duk da alkawarin da hukumomi suka dauka na dage haramci a kan gudanar da zanga zanga a kasar, haramci da ya fara aiki tun cikin shekarar 2017

Tace kafin zaben kasar mai muhimmanci a ranar 23 ga watan Disemban wannan shekara, muna kira ga hukumomin Congo da su mutunta 'yancin fadar albarkacin bakin jama’a da shirya tarukan lumana. Ta kuma ce duk wani zargi da aka yiwa 'yan sanda da jami'an tsaro a kan amfani da karfi fiye da kima, yakamata a yi bincike akai da zummar hukunta masu laifi.

Shamdasani tace an kashe wani dan fafutukar siyasa a kudu maso gabashin kasar, kana an kama sama da masu zanga zanga 140 tun cikin watan Agusta, galibi a cikin samame da jami’an tsaro suka kai.

Ta kara da cewa ana daure mutane da laifukan bijirewa hukuma, da kafa kungiyoyi ba bisa ka’ida ba, da fahse fashe da kone kone da kuma zagin dan sanda. Ta fadawa Muryar Amurka cewa an riga an sako wasu mutane daga gidan yari, lamarin da ta kwatanta da labari mai dadi.

Tace koda yake tsaresu da aka yi bisa dalilin fadar ra’ayinsu da kuma shirya zanga zanga, wani babban kuskure ne, musamman yayin da zabe ke karatowa. Hakan na aikewa da sako ga kungiyoyin fafutuka da jami’iyyun adawa cewa ba za a lamunta da ayyukansu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG