Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Za Ta Kafa Hukuma Ta Musamman Don Dakile Yaduwar Makamai


Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))
Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Majalisar Dokokin Najeriya ta jaddada kokarinta na hana yaduwar makamai domin dakile duk wani yunkuri na ta'addanci baki daya a kasar.

Wannan ya bayyana ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta saurari ba'asin masu ruwa da tsaki, a wani yunkuri na kafa wata hukuma ta musamman da za ta rika sa ido kan yadda ake mu'amala da makamai a Najeriya.

Wanan mataki da Majalisar ta dauka na kokarin kafa hukuma ta musamman da za ta dakile yaduwar makamai a tsakamin jama'ar kasa, sannan kuma ta sa ido akan yadda za a yi mu'amala da makaman, kuduri ne da ke cikin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da ta ECOWAS akan yaduwar makamai.

Shugaban Kwamitin kula da Harkokin Leken Asiri na Tsaron Kasa, Ibrahim Abdullahi Gobir, ya yi karin haske akan yadda hukumar za ta kafu. Ya ce za su tabbatar da cewa duk wanda ya shigo da makamai ba a hukumance ba, za a kama shi, tare da hadin gwiwar hukumomin shige da fice, DSS, Yan Sanda da dai sauransu.

Ganin cewa akwai matukar bukatar samun sahihan bayanan sirri a yanzu da lokacin da hukumar za ta fara aiki gadangadan, Aminu Saleh Jaji tsohon dan Majalisar Wakilai kuma wanda ya taba shugabantan kwamitin kula da harkokin tsaro da leken asiri, ya yi bayani cewa hukumar leken asirin kasa ta na da kwarewar da za ta bada gudumawa wajen samo bayanan sirri.

Ana sa ran Kwamitin Tsaro da Leken Asirin kasa na Majalisar Dattawa zai hada kai da takwaran aikinsa na majalisar wakilai wajen daidaita dokar domin majalisar kasa ta amince da ita.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
XS
SM
MD
LG