Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokin Najeriya Ta Bayyana Kudirin Ta Na Kafa Dokar Sa Ido Ga Kungiyoyi Masu Zaman Kansu


Majalisar Dokokin Najeriya ta bayyana aniyar ta ta yin wata doka da za ta sa ido akan aiyukan kunyiyoyi masu zaman kansu, kama daga yadda suke yin rajista da yadda suke samun kudaden shiga da ma yadda suke aiwatar da kudaden shiga.

Tuni dai aka yiwa kudurin dokar karatu na biyu a majalisar wakilai, harma an fara shirin bude dandalin sauraren ba’asin ‘yan kasa kan alfanun yin wannana doka ko kuma akasin hakan.

Rahotanni sun bayyana cewa a cikin kasashe masu tasowa Najeriya, ce kasa ta uku dake da yawan irin wadannan kungiyoyi masu zaman kansu. Auwal Musa Ramsan Jani, shine shugaban gamaiyar kungiyoyin kare hakkin jama’a a yankin Afirka ta yamma, ya bayyana cewa yunkurin da majalisar ke kokarin yi abin takaici ne a dai dai lokacin da majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyi ke kokarin budewa kungiyoyi hanyar inganta cudanya da gudumuwar su wajan kawo ci gaba a duniya.

Dan majalisar wakilai Ahmed Babba Kaita, ya bayyana cewa Najeriya, kasa ce mai cin gashin kanta dan haka wajibi ne a rika samun sauyi nigari a dabi’unta da kuma dokokinta, dan haka bai kamata majalisar dinkin duniya ta sa baki cikin al’amurran kasa ba. Ya kuma kara da cewa dokar zata bukaci kungiyoyin su bayyana yadda suke samun kudaden shiga da yadda suke kashe kudaden ne kawai.

Shima Barista Mainasa Kogo Ibrahim, babban lauya kuma mai Nazari akan al’amurran da suka shafi tsarin mulki ya bayyana matsayar dokokin tsarin mulkin Najeriya dangane da irin hurumi da dokokin da kungiyoyi masu zaman kansu zasu iya mora a kasa.

Domin Karin bayani, saurari rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG