Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa


Issoufou Mahammadou, shugaban kasar Nijar

A shakarar 2011 ne shugaban kasar Nijar Issoufou Mahammadou ya kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a wani yunkuri na tunkarar masu sama da fadi da wawure dukiyar kasa.

Abun da ya hana hukumar yin aikinta yadda ya kamata shi ne rashin samun doka daga majalisa da zata bata bakin cizo da kafafuwan tsayawa a hukumance, lamarin da ya sha dabaibaye ayyukanta.

Gwamnatin Issoufou Mahammadou ta aika da kudurin doka majalisar da zai halarta hukumar domin tayi aikinta na ceto kasar daga cin hanci da rashawa, handama da sama da fadi.

Masu rinjaye a majalisar sun bada hadin kai har aka samu kuri'un goyon baya dari da takwas da suka tabbatar da hukumar. Audu Magawata na jam'iyyar dake mulki PNDS yayi karin haske kan abun da ya faru a majalisar. Yace yau hukumar na iya bincike ta kai abun da ta gano wa shugaban kasa kafin a san abun da ya kamata a yi.

Amma 'yan adawa a majalisar sun nuna ko oho da dokar saboda a cewarsu babu wani cikakken sauyin da ta zo dashi saboda hukumar zata cigaba da zama a karkashin fadar shugaban kasa

Alhaji Lawali Ibrahim dan majalisa na jam'iyyar MNRD yace 'yan hukumar zasu zama 'yan amshin shatan gwamnati ne. An nadasu ne domin su biyawa gwamnati bukata. Hukumar da aka ce ta binciki masu sama da fadi da dukiyar kasa kuma har sai an bata umurni, wato tana karkashin ikon wani bai dace ba. Yace 'yan majalisar sun bi zuciyarsu ne kawai.

Amma shugabar kwamitin majalisar dake yaki da cin hanci Hajiya Halima Mamman tace abun da ta sani kawo yanzu shugaban kasa ko na kusa dashi bai taba ba hukumar umurin ta kama wani ba ba akan ka'ida ba.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG