Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Zamfara Tana Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar


Mahdi Aliyu Gusau, Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mika takardar sanarwar fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Mahadi Ali.

Wannan ba shi ne karo na farko da a ke yunkurin tsige Mahadi daga kujera ba tun lokacin da ya ki bin gwamna Bello Matawalle su sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki a tarayya.

Cikin tuhumar da a ke yi wa Mahadi wanda dan Janar Ali Gusau ne ana zarginsa da azurta kansa da kudin gwamnati da rashin sauke nauyin tsarin mulki da aka dora ma sa.

In za a tuna gwamna Matawalle ya tattara dukkan gwamnatin sa ya shigar da ita APC; bayan tun farko kotun koli ta ba su damar cike dukkan kujerun APC a sanadiyyar soke zaben jihar.

A tarihin siyasar Najeriya wannan ba shi ne karo na farko da aka tsige mataimakin gwamna a irin wannan yanayi ba. A baya gwamnatin tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda ta tsige marigayi tsohon mataimakin gwamnan jihar Garba Gadi bayanda aka sami sabani tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

XS
SM
MD
LG