Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Kyawun Yanayin Samaniya Ya Hana ni Ziyara zuwa Jihar Zamfara - Shugaba Buhari


Shugaban Muhammadu Buhari
Shugaban Muhammadu Buhari

Kalubalen rashin kyawun yanayi ya dakatar da shugaba Buhari daga ziyartar jihar Zamfara daga Sokoto don jajantawa al’ummar jihar bisa yawan hare-hare ‘yan bindiga da kan yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Shugaban wanda ya shiga Sokoto da duba kamfanin siminti na BUA, ya so ya zarce Zamfara da jirgi mai saukar angulu amma rashin kyawun yanayi ya sa ya janye.

Bayan dawowar sa Abuja, shugaban Muhammadu Buhari ya yi jawabi a faifan sako na bidiyo da na radiyo inda ya bayyana uzurin da ya sa bai shiga Zamfara ba, ya na mai cewa nan gaba in ya samu lokaci zai kai ziyarar.

Shugaban ya godewa gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun da yanda ya shirya tarba amma hakan bai tafi yanda a ke so ba don yanayi.

A baya dai an sha gorantawa shugaba Buhari kan rashin ziyartar Sokoto da Zamfara da ‘yan bindiga kan ci Karensu ba babbaka.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG